Sultan Shuwa Arab, Lagos

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sultan Shuwa Arab Lagos Alh. Jibril Yahya Ibrahim



Sarkin Shuwa Arab na Lagos
Alhaji Jibril Yahya Ibrahim

Gabatarwa

Babban sarkin Shuwa Arab na Jahar Lagos, Alhaji Jibril Yahya Ibrahim, makiyayi ne sannan kuma ƙwararre a harkar sufuri. Shi ne mutumin farko da ya fara shugabantar dukkanin al’ummar Shuwa Arab da ke Lagos a dunƙule a matsayin Sultan.

Mutum ne shi mai haƙuri; iya tafiyar da harkokin jama’a; barkwanci da sauran kyawawan halaye ababen yabawa. Yana matuƙar son zaman lafiya da haɗin kai. “Shugabancin Alhaji Jibril yana cigaba da zama alheri da kuma ƙara ƙaimi. Ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen inganta jindaɗi da walwalar al’ummar Shuwa Arab. Kuma jagorancinsa ya kawo zaman lafiya, haɗin kai da kuma cigaba tsakanin jama’arsa da kuma sauran ƙabilu. Jama’armu da suke zaune suna gudanar da halastaccen kasuwanci a Yammacin Ƙasar nan, mutane ne masu zaman lafiya da kuma bin doka-da-oda” in ji Khurso Addudu, babban sakataren masarauta a cikin zantawar su da jaridar The Sun ta ranar 29 ga watan Agustan shekarar 2019.

Wannan rubutu da ka ke karantawa, zai yi taƙaitaccen bayani sannan kuma gamsasshe game da wannan babban Sarki na Shuwa Arab da ke Jahar Lagos.

Haihuwa

An haifi Alhaji Jibril Yahya Ibrahim a garin Maiduguri cikin watan goma na shekarar 1959. Shuwa Arab ne shi ta ɓangaren Mahaifinsa Alhaji Yahya ɗan Alhaji Ibrahim dukkaninsu haifaffun Maiduguri. Ta ɓangaren mahaifiya kuma, Alhaji Jibril Bafullace ne. Sunan mahaifiyarsa a Fullance Jumba, amma an fi kiranta da Ammabuwa; wadda kalma ce da ke da ma’ana ta mahaifiyar babanta a cikin harshen Shuwa Arab, kasancewar ta takwara ga kakarta; wato an saka mata suna irin na kakarta ta wajen mahaifinta.

Karatu

Kamar yadda aka saba tarbiyyantar da dukkan ɗan Musulmi, Alhaji Jibril ya buɗi ido ne da karatun Alƙur’ani da kuma kiwon dabbobi saboda zamowar mahaifansa makiyaya. Sai dai duk da haka, Alhaji Jibril da kansa ya riƙa zuwa darrusan makarantun manya domin koyon karatu da rubutun boko.

Gogayyar Aiki

Kasancewar Alhaji Jibril ɗan ƙabilar Shuwa Arab, ya samu kansa a cikin sana’ar kiwon dabbobi tun yana ƙarami, sana’ar da ya girma a cikinta har ya koma fataucin shanu daga Arewaci zuwa Kudancin Najeriya.

Alhaji Jirbil Yahaya Ibrahim ya zama shugaban Kasuwar Shanu ta Agege a zamanin gwamnan Lagos Kanar Buba Marwa har tsawon shekaru biyar.  Daga nan kuma sai ya bari ya sake kafa kasuwar shanu ta Isheri.

Iyali

Alhaji Jibril Yahya Ibrahim mutum ne magidanci mai mata biyu rayayyu a yanzu haka. Ya yi aurensa na farko a shekarar 1973. Bayan rasuwar matarsa ta farko mai suna Amina, sai ya auri wata mata mai suna Hajja, wadda suka zauna da ita tsawon shekaru huɗu. Bayan rabuwar su da Hajja ya sake auren mata biyu waɗanda duk suka rasu. Sai kuma yanzu da yake zaune da matansa biyu; Ajashe da Hauwa da kuma ‘ya’ya da suka haura ashirin.

Zamowarsa Sarki

Alhaji Jibril Yahya Ibrahim ya zama sarkin Shuwa Arab na Lagos mai muƙamin Sultan wanda kuma shi ne ya buɗe wannan masarauta.

Wani kwamati mai mutum goma sha ɗaya da aka kafa a cikin shekarun 70s, shi ne ya fitar da Alhaji Jibril Yahya a matsayin sarkin Shuwa Arab na Yankin Kudu Maso-Yammacin Najeriya, yankin da ke cikin farfajiyar Ƙasar Yarabawa.

Tun da farko, an samu shugabannin al’ummar Shuwa Arab da suke yi wa kansu laƙabi da Janar har sama da ashirin, abin da ya haifar da shugabancin ta-ci-barkatai a tsakanin al’ummar Shuwa Arab mazauna yankin. Daga ƙarshe, manyan mutane irin su marigayi Alhaji Girema, Alhaji Gaji Abubakar, da sauransu suka shawarci al’ummar da cewa su daure su fitar da shugabanci guda ɗaya a tsakaninsu.

Gazawar waɗancan Jana-Janar wajen fitar da shugaba ɗaya a cikinsu, shi ne abin da ya haifar da kafuwar wancan kwamati da aka ambata. Da kwamatin ya zauna domin fitar da mutumin da zai jagoranci al’ummar Shuwa da ke Lagos da kewaye tare da kiyaye cewa ya zama nagartacce mai siffofin yabawa, sai kwamatin ya fitar da shi Alhaji Jibril Yahya Ibrahim wanda kuma suaran jama’a suka amince ba tare da tababa ba, kamar yadda Alhaji Ahmadu Turakin Masarautar Shuwa Arab ya gaya mana a cikin tattaunawar mu da shi wanda kuma shi mamba ne a wancan kwamati mai wakilai goma sha ɗaya. Mun yi wannan tattaunawa a Ranar Lahdi, 1/3/2020 a Fadar Masarautar Shuwa Arab da ke lamba 2, Esther Close, ƙaramar hukumar Oluti Amuwo Odofin, a Jahar Lagos.

Manazarta:


Udemba T. (2019). Lagos Shuwa-Arab community reaffirms loyalty to leader. Jaridar The Sun ta ranar 29/8/2019. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.sunnewsonline.com/lagos-shuwa-arab-community-reaffirms-loyalty-to-leader/

Tattaunawa da Sultan Jibril Yahya Ibrahim a Fadarsa da ke Lagos a Ranar Asabar 29/2/2020

Tattaunawa da Alhaji Ahmad Turakin Masarautar Shuwa Arab ta Lagos a Fadar Masarautar da ke Lagos a Ranar Lahdi 1/3/2020  




Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub